Bakonmu a Yau

An samu rarrabuwar kai tsakanin lauyoyin Najeriya kan janye gayyatar da suka yiwa El Rufa'i

Sauti 03:36
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i. RFI Hausa / Aminu Sani Sado

Dambarwar da ta biyo bayan janye gayyatar da aka yiwa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai domin yiwa taron kungiyar lauyoyin Najeriya jawabi yanzu haka na neman raba kungiyar gida biyu, ganin yadda kungiyar lauyoyi Musulmi suka bukaci daukaci ‘yayan su su kauracewa taron.Dangane da wannan mataki Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Barista Lawal Ishaq, lauya mai zaman kan sa, kuma ga bayanin da yayi mana akan wannan mataki.