Najeriya

'Yan bindiga sun sace jami'an tsaro a Kaduna

'Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'an tsaro 2 a Kaduna.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da jami'an tsaro 2 a Kaduna. Information Nigeria

‘Yan bindiga a Kaduna sun sace mutane hudu cikinsu har da jami’in dan sanda 1, da na Civil Defence guda, yarinya mai shekaru 14, da kuma wani mutum.

Talla

Jami’an tsaro sun ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutanen ne bayan harin da suka kaiwa gidajensu a Maraban Rido dake karamar hukumar Chikun dake Kadunan, a daren ranar Alhamis da ta gabata.

Wadanda suka tsira daga farmakin sun ce maharan sun afkawa jama’a ne cikin tsakar dare, tare da budewa mutane wuta.

Koda dai rundunar ‘yan sanda bata ce komai kan lamarin ba, kakakin rundunar tsaro ta Civil Defence a Kaduna Orndiir Terzungwe, ya tabbatar da harin ‘yan bindigar.

Kakakin rundunar ta Civil Defence ya ce tuni suka soma farautar maharan.

Harin ya zo ne kwanaki 4, bayanda wasu yan bindigar suka sace wani adadin da ba a kai ga tantancewa ba, na dalibai a jihar ta Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.