Najeriya

ICPC ta soma bincikar jami'an NDDC kan zargin sace naira biliyan 5

Headikwatar hukumar ICPC mai yakar laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya.
Headikwatar hukumar ICPC mai yakar laifukan cin hanci da rashawa a Najeriya. Photo Credit: icpc.gov.ng

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, to soma bincikar manyan jami’an hukumar raya yankin Niger Delta NDDC, kan zarge-zargen halasta kudaden haramun da kuma sace makudan kudaden da gwamnati ta ware don yakar annobar coronavirus.

Talla

A jiya asabar kakakin hukumar ta ICPC Azuka Ogugua yace tuni manyan darakatocin NDDCn suka gurfana gabansu, inda suke amsa tambayoyi, kan tuhume-tuhumen da ake musu.

Ogugua yace binciken da suke a halin yanzu ya maida hankali ne kan zargin da ake wa manyan jami’an hukumar raya yankin Niger Deltan na karkatar da naira biliyan 5 da kusan rabi, da aka ware domin sayen kayayyakin baiwa ma’aikatan lafiya kariya daga cutar coronavirus, tare da tallafawa jihohi 9 wajen dakile annobar.

Kakakin hukumar yaki da laifukan rashawar ta ICPC, ya kara da cewar, sun kuma kaddamar da bincike kan batan dabon miliyoyin nairar da aka baiwa hukumar yankin Niger Deltan ta NDDC domin tura ma’aikatanta daukar horo a kasashen ketare a lokacin da annobar coronavirus ta dakatar da zirga-zirga a duniya, shirin da har yanzu ba a aiwatar ba.

Zalika manyan jami’an na NDDC za su bada bahasi kan yadda suka yi da miliyoyin kudaden da aka tsara za a baiwa dalibai a yankin na Niger Delta, domin karo karatu a kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.