Wasanni

Dole Messi ya biya Barcelona euro miliyan 700 kafin rabuwa da ita - La Liga

Kaftin din Barcelona Lionel Messi.
Kaftin din Barcelona Lionel Messi. AFP

Hukumar La liga ta Spain ta haifar da cikas ga aniyar kaftin Barcelona Lionel Messi da ya sha alwashin rabuwa da kungiyar, bayanda hukumar ta La Liga ta yanke hukuncin cewa dole gwarzon dan wasan, ko kuma kungiyar da zai koma, su biya Barcelona euro miliyan 700 kafin samun damar rabuwa da ita.

Talla

A makon jiya Messi ya shaidawa Barcelona aniyar sa ta sauya sheka, ta hanyar kawo karshen yarjejeniyarsa da ita mai sauran shekara guda. Yayin gabatar da bukatar Messi yace zai yi amfani da sashin dokar dake cikin yarjejeniyarsa da Barcan, da ya bashi damar komawa wata kungiya a matsayin dan wasa mai zaman kansa a karshen kowace kakar wasa.

Sai dai Barcelona tace tun cikin watan Yulin da ya gabata wa’adin damar da Messi ke da ita ta kare, yayinda su kuma lauyoyin kaftin din suka bukaci yi masa adalcin cewar, kakar wasa ta bana ta zarce watan Yuli da aka tsara zata karkare ne, saboda annobar coronavirus.

Ana tsaka da wannan takaddamar ce, hukumar La Liga ta marawa Barcelona baya kan tsayuwar gwamen jakin da Barcelonan tayi kan cewa dole Messi ya biyata zunzurutun kudi euro miliyan 700 a matsayin toshin sakin da zai mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.