Mawakin Kano da ya yi batanci ga Annabi ya daukaka kara kan hukuncin kisa

Matashin Mawakin nan na jihar Kano Yahaya Aminu Shariff, da wata Kotun Shari'ar Musulunci ta yankewa hukuncin kisa a jihar bisa samun sa da laifin batanci ga manzon tsira Annabi Muhammadu (SAW) ya daukaka kara zuwa babbar kotun jihar Kanon, yana mai kalubalantar hukuncin farko.

Tambari kotun shari'a  ta Najeriya.
Tambari kotun shari'a ta Najeriya. sharia court of Nigeria
Talla

A ranar Alhamis din nan ne matashin mai shekaru 22 ya daukaka karar kwanaki kalilan kafin cikar wa'adin kwana 30 da kotun ta debe kafin aiwatar da hukuncin kisan, yana mai cewa kotun shari’ar bata cikin tsarin mulki da dimokradiya.

Tuni gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya shirya tsaf don sanya hanna kan hukuncin na kisa kamar yadda doka ta tanada, idan har wa’adin daukaka karar ya zarce.

A ranar Laraba shahararren lauyan nan mai kare hakkin bil adama Cif Femi Falana ya yi zargin cewa kotun ta Kano ta hana takardun shari'ar, wadanda za su ba da damar daukaka kara, duk da shafe kusan mako biyu ana neman takardun shari'ar, to sai dai a Alhamis din nan an sanar da mikawa Falanan takardun.

Sai dai hukumomin shari’ar ta Kano sun musanta zargin shaharerren lauyan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI