Najeriya

Tsoho ya yiwa yarinya ‘yar shakara 4 fyade a Masallaci

Matsalar yi kananan yara fyade na ciwa al'ummar Najeriya tuwo a kwarya
Matsalar yi kananan yara fyade na ciwa al'ummar Najeriya tuwo a kwarya Reuters

A Najeriya an samu rudani a wani Masallaci dake garin Bauchi, bayan kama wani mutum yana lalata da wata yarinya ‘yar shakara 4, abinda ya tunzura ‘yan unguwa suka rufa shi da duka, kafin ‘yan sanda su kwace shi da kyar.

Talla

Wannan dai ba shi ne karo na farko da irin haka ke faruwa ba a sassan Najeriya, matsalar ya a watannin baya bayan nan ta zama gama gari.

Daga Bauchi, wakilinmu Shehu Saulawa ya aiko mana da rahoto.

Rahoto kan yadda tsoho ya yiwa yarinya ‘yar shakara 4 fyade a Masallaci

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.