Najeriya: Kungiyar ma'aikatan lafiya ta baiwa 'ya'yanta umarnin soma yajin aiki
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kungiyar ma’aikatan lafiya ta Najeriya JOHESU ta baiwa daukacin ‘ya’yanta umarnin soma yajin aiki daga karfe 12 na daren yau Lahadi.
Cikin sanarwar da ta fitar a yau Lahadi, kungiyar ma’aikatan lafiyar tace kafin shiga yajin aikin, sai da ta baiwa gwamnatin Najeriya wa’adin mako 1, da ta soma daukar matakan warware matsalolin da suka yiwa fannin lafiya, ciki harda karancin kayan aiki, rashin biyansu kudaden alawus na yakar annobar coronavirus, amma gwamnatin ta nuna halin ko in kula.
Karin kan bukatun kungiyar ma’aikatan lafiyar na Najeriya JOHESU kuma shi ne gayara tsarin albashin da ake biyansu kamar yadda manyan kotunan klasar suka bada umarni a shara’o’in da suka sauarara.
A ranar 7 ga watan Satumba kungiyar likitocin Najeriya masu neman kwarewa suka suka shiga yajin aiki kan rashin kyawun yanayin gudanar da ayyukansu, da kuma karancin albashi a daidai lokacin da suke taka rawa wajen yakar annobar coronavirus a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu