Buhari-Najeriya

Buhari ya gargadi 'yan siyasa kan tayar da hankali a zaben jihar Edo

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter/@BashirAhmad

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi 'yan siyasa da 'yan takarar zaben Gwamnan Jihar Edo da za’ayi a karshen wannan mako tare da jami’an tsaro da su tabbatar da bin doka da oda don kaucewa tashin hankali.

Talla

A sakon da ya aikewa jama’ar jihar da suka kunshi masu kada kuri’u da jami’an zabe da kuma Jam’iyyun siyasa, Buhari yace har yanzu yana kan bakar san a tabbatar da karbabben zabe ba tare da samun tashin hankali ba, saboda haka ba zai amince da masu bukatar hana ruwa gudu daga kowanne bangare ba.

Shugaban kasar yace yana bukatar ganin an inganta hanyoyin dimokradiya a Najeriya, amma hakan zai samu ne kawai idan Yan siyasa suka kaucewa aniyar su ta samun nasara ta kowacce hanya.

Buhari yace bukatar samun nasara ta kowacce hanya na barazana ga sahihancin zabe, saboda ganin yadda masu ruwa da tsaki ke fifita lashe zaben maimakon tabbatar da sahihancin sa.

Shugaban ya bukaci ‘yan siyasa da Jam’iyyun su da su mutunta dokokin zabe, yayin da ya bukaci jami’an zabe da na tsaro da su kaucewa magudi domin kare mutuncin su.

Buhari yace daya daga cikin tarihin da yake son bari shine na gudanar da karbabben zaben da jama’a zasu yaba lokacin da ya bar ofishin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.