Najeriya

Direbobin tankar mai sun dakatar da jigila daga Legas zuwa arewacin Najeriya

Daya daga cikin motocin tanka masu jigilar dakon mai a Najeriya.
Daya daga cikin motocin tanka masu jigilar dakon mai a Najeriya. Daily Trust

Kungiyar direbobin motocin tanka masu dakon man fetur ta baiwa ‘ya’yanta umarnin dakatar da jigilar man daga birnin Legas zuwa sassan arewacin kasar daga yau Alhamis har sai abinda hali yayi.

Talla

Shugaban kungiyar direbobin tankar na Najeriya Otumba Oladiti yace tilas ne su yanke hukuncin, saboda matakin gwamnatin Niger na haramtawa dukkanin manyan motoci bin hanyoyin da suka ratsa ta cikin garin Minna, babban birnin jihar.

Tun ranar 15 ga watan Satumban nan gwamnatin Jihar ta Niger ta bada umarnin rufewa manyan motocin dakon kayan hanyoyin da suka ratsa garin na Minna, da zummar soma aikin gyara hanyoyin. Sai dai kungiyar direbobin tankokin man sun ce har zuwa lokacin wallafa wannan labara ba a soma aikin ba.

A cewar kungiyar direbobin tankar, hanyar da yanzu ta rage musu itace wadda ta tashi daga Bidda zuwa Agai zuwa Lapai sai kuma Lambata, sai dai rashin kyawun hanyar yayi muni matuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI