Najeriya

NLC ta baiwa gwamnati mako 2 ta janye karin farashin mai da lantarki

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya Ayuba Philibus Wabba, yayin jagorantar zanga-zangar adawa da gwamnatin Najeriya a Abuja.  9/2/2017.
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya Ayuba Philibus Wabba, yayin jagorantar zanga-zangar adawa da gwamnatin Najeriya a Abuja. 9/2/2017. REUTERS/Afolabi Sotunde

Kungiyar kwadagon Najeriya NLC, ta baiwa gwamnatin kasar wa’adin makwanni 2 da ta janye karin farashin litar mai, da kuma lantarkin da ta yi, ko kuma ta fuskanci gagarumar zanga-zanga a daukacin sassan kasar.

Talla

Hadaddiyar kungiyar kwadagon ta NLC ta fitar da sanarwar ce bayan shafe sa’o’i shugabannin kwamitin gudanrwarta na taro kan batutuwan karin farashin litar man da kuma karin akalla kashi 50 na kudin samun hasken lantarki.

Shugaban kungiyar Ayuba Wabba yace wa’adin makwanni biyun ya soma aiki ne nan take daga ranar Laraba, kuma zuwa ranar 28 ga watan Satumba za su jagoranci ‘yan Najeriya wajen soma zanga-zangar adawa da gwamnati a daukacin kasar, muddin gwamnatin ta ki janye karin farashin man da kuma lantarkin da ta yi.

Ranar Talatar da ta gabata, aka shafe sa’o’I akalla 8 ana tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Ministan Kwadago Chris Ngige da kuma shugabannin kungiyar Kwadagon kasar ta NLC, sai dai an gaza cimma maslaha tsakanin bangarorin, inda gwamnati ke cewa kamata yayi ma ‘yan Najeriya su gode domin kuwa ba don matakan da ta dauka ba, farashin litar man ka iya zarta farashin da aka kara na naira 160.

Yanzu haka dai kungiyar ma’aikatan lafiyar Najeriya na cigaba da yajin aikin da suka shiga tun daren lahadin da ta gabata, bayan da suka zargi gwamnati da kin amsa bukatunsu na warware matsalolin da suka yiwa fannin lafiya, ciki harda karancin kayan aiki, da rashin biyansu kudaden alawus na yakar annobar coronavirus.

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Kwamrade Nasir Kabir mataimakin sakataren kungiyar kwadagon ta NLC na kasa, ya yi karin bayani kan matakin da suka dauka.

Kwamrade Nasir Kabir mataimakin sakataren kungiyar NLC kan wa'adin da suka baiwa gwamnatin Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI