Najeriya

Za mu ci gaba da goyon bayan Dimokradiyya a kasashen ECOWAS- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore RFI Hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce kasar za ta cigaba da goyan bayan dorewar dimokiradiya a yankin Afirka ta yamma wajen ganin kasashen da ke yankin sun mutunta kundin tsarin mulkin da su ke amfani da su.

Talla

Buhari ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore da ya ziyarce shi don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu da kuma yankin ECOWAS.

Shugaban Najeriyar ya ce suna sanya ido sosai kan halin da ake ciki a kasashen da ke shirin zabuka, kuma sun fahimci kasashen da ake zaman lafiya da kuma wadanda ake fuskantar tashin hankali, yayin da ya bayyana aniyar taimakawa masu fuskantar zabubbuka.

Shugaba Kabore da ya jagoranci kwamitin tattalin arziki da kasuwanci da kuma zuba jari na ECOWAS ya ce ya ziyarci Buhari ne domin tattauna wasu batutuwa da suka shafi yankin da suka hada da hukumar hadin kai tsakanin Burkina Faso da Najeriya da kuma matsalar kasuwancin da ake fuskanta tsakanin Najeriya da Ghana da Benin da Nijar domin samo maslaha.

Kabore ya yabawa Buhari kan yaki da ‘yan ta’adda da kuma jagoranci wajen tinkarar annobar korona.

Dangane da halin da ake ciki a Mali, shugaban Burkina Faso ya bayyana fatar ganin taron da akayi a Ghana ya haifar da daa mai ido domin samun dawamammen zaman lafiya a Afirka ta Yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI