Najeriya

Gwamnati ta nemi afuwa kan umarnin bada sabbin bayanan asusun ajiyar bankuna

Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja dake Najeriya. 22/1/2018.
Hedikwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja dake Najeriya. 22/1/2018. REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Gwamnatin Najeriya ta nemi afuwar al’ummar kasar dangane da wani umurnin da ta bayar wanda ya bukaci duk wani mai ajiya a banki da yaje ya sake gabatar da sabbin bayanai domin tantance shi.

Talla

Wata sabuwar sanarwar da hukumomin kasar suka bayar yau juma’a kasa da sa’oi 24 bayan wadda suka bayar jiya, ta nemi jama’a da su yafe mata kan kuskuren da tayi, inda take cewa sanarwar bata shafi daukacin jama’ar kasa ba.

Hukumar tara kudaden shigar kasar tace tayi kuskure wajen sanarwar da ta gabatar jiya, inda tace bukatar cika takardun ko gabatar da bayanan ya shafi masu asusun ajiya a kasashen waje ne domin tantance kudaden harajin da ya dace su dinga biya.

Tuni dai umurnin ya gamu da suka daga sassa daban daban na al’ummar kasar wadanda ke ganin cewar matakin ya saba ka’ida ganin irin bayanan da hukumomin gwamnati da na ‘yan kasuwa ke da shi kan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.