Najeriya-Kaduna

'Yan bindiga sun sace mutane 7 a Barakallahu

Matsalar satar mutane na karuwa a sassan ciki da wajen jihar Kaduna a baya bayan nan.
Matsalar satar mutane na karuwa a sassan ciki da wajen jihar Kaduna a baya bayan nan. The Guardian Nigeria

Akalla mutane 7 ‘yan bindiga suka sace a unguwar Barakallahu dake karamar hukumar Igabin jihar Kaduna a daren wayewar garin Juma’ar nan.

Talla

Wadanda suka shaida aukuwar lamarin sun ce maharan sun afkawa yankin ne da misalin karfe 1 na daren ranar ta Juma’a, inda suka rika bi gida-gida suna zakulo mutanen da suka sace.

Bayanai sun ce mutane 5 daga cikin wadanda ‘yan bindigar suka sace iyali ne guda na wani mazaunin yankin Abdulsalam Haruna, da suka hada da matar aure da ‘ya’yanta 4.

Kaduna dai na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka hada da Sokoto, zamfara, Katsina da kuma Nasarawa, dake fama da hare-haren ‘yan bindiga duk da cewar, rundunonin tsaron kasar na cigaba da kaddamar da farmaki kan sansanonin ‘yan bindigar a dazukan dake tsakanin jihohin, gami da kame masu taimaka musu.

A alhamis din da ta gabata, wasu gungun ‘yan bindigar a jihar Sokoto suka kashe ‘yan sanda 2 da manoma 5 a wasu hare-hare.

Yayin farmakin gungun ‘yan bindigar da ya kunshi mutane kimanin 100 ne sanye da kakin soja suka kai samame kan osfishin ‘yan sanda dake kauyen gidan Madi a jihar ta Sokoto inda suka kashe jami’ai biyu, tare da kwashe tarin makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.