Najeriya

Al'ummar Edo na kada kuri'ar zaben sabon gwamna

Takardar kada kuri'a a zabukan Najeriya.
Takardar kada kuri'a a zabukan Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Yau asabar zaben gwamnan jihar Edo ke gudana a Najeriya, inda za a fafata tsakanin Jam’iyyar PDP mai mulki da APC da ta rasa kujerar Jihar.

Talla

Gwamna Godwin Obaseki da ya sauya sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP na neman wa’adi na biyu, yayin da Fasto Eze Iyamu da yayi takara da Obaseki shekaru 4 da suka gabata a karkashin Jam’iyyar PDP ya koma APC, ya kuma tsaya mata takara.

Akwai dai karin wasu Yan takara daga Jam’iyyu daban daban a zaben na yau, sai dai karawar da za a yi tsakanin Obaseki da Iyamu ce tafi daukar hankali.

Hukumar zaben Najeriya tace akalla mutane miliyan 1 da dubu 720 take sa ran za su kada kuri’a a zaben gwamnan na Edo, yayinda wasu akalla dubu 483 da 796 ba za su samu damar kada kuri’un nasu ba saboda wasu dalilai, ciki har da rashin karbar katunansu daga hannun hukumar zaben.

Tuni dai fargaba ta mamaye jama’ar Jihar ta Edo, ganin yadda aka yi ta samun tashin hankali lokacin yakin neman zaben, abinda ya sa aka kara yawan jami’an tsaro da kuam sanya ‘yan takarar sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya domin tabbatar da ganin an yi zaben ba tare da tashin hankali ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.