Najeriya-Kaduna

Allah ya yiwa Sarkin Zazzau rasuwa

Mai martaba Sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris
Mai martaba Sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris Twitter/@GovKaduna

Rahotanni daga jihar Kaduna dake tarayyar Najeriya, sun ce Allah ya yiwa mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris rasuwa da safiyar yau lahadi, 20 ga watan Satumba a birnin Abuja.

Talla

A farkon wannan shekara, Sarkin yayi bikin cika shekaru 45 kan karagar masarautar ta Zazzau.

Marigayin shi ne Sarkin yankan masarautar zazzau na 18 daga kabilar Fulani, wanda ya rasu yana da shekaru 84.

Majiyoyi daga masarautar sun ce tun a ranar Juma’a aka garzaya da marigayin zuwa asibiti, inda bayan gajeruwar jinya ya rasu.

A 1975 Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris ya soma mulkin masarautar har zuwa yau lahadi 20 ga watan Agustan 2020, lokacin da Allah ya karbi kayansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.