Najeriya

'Yan Najeriya na dakon sakamakon zaben gwamnan Edo

Wani jami'in hukumar zaben Najeriya, yayin kidayar kuri'u
Wani jami'in hukumar zaben Najeriya, yayin kidayar kuri'u REUTERS/Adelaja Temilade

'Yan Najeriya na cigaba da jiran sakamakon zaben gwamnan jihar Edo da ya gudana a jiya asabar, wanda jami’ai ke cigaba da kidayar kuri’un da aka kada cikinsa.

Talla

‘Yan takara 14 ne dai suka fafata kan kujerar gwamnan, sai dai hammaya tsakanin gwamna mai ci Godwin Obaseki na Jam’iyyar PDP da kuma Fasto Ize-Iyamu na APC ce tafi daukar hankali, wadanda sakamakon farko da ya fita ya nuna cewa dukkaninsu sun lashe mazabunsu.

Bayan kada kuri’arsa gwamna Godwin Obaseki, ya bayyana mamaki gami da kaduwa kan bata lokacin da ake yi kafin na’urar tantance mai kuri’a ta Card Reader tayi aikinta duk da ikirarin hukumar zabe na daukar matakan inganta ayyukanta, abinda yace ba shakkah zai takaita adadin mutanen da za su kada kuri’unsu.

Sai dai a nasa bangaren dan takarar APC Ize-Iyamu yace bashi da wani korafi kan yadda zaben ya gudana.

Zaben gwamnan jihar ta Edo dai, shi ne babban zabe na farko da ya gudana a Najeriya tun bayan da annobar coronavirus da barke a kasar daga farkon wannan shekara.

Rahotanni sun ce zaben gwamnan na Edo ya gudana cikin kwanciyar hankali a mafi akasarin sassan jihar, sabanin yadda wasu ke fargabar barkewar tashe-tashen hankula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.