Najeriya

Godwin Obaseki Ya Lashe Zaben Gwamnan Edo Najeriya

Wata baiwar Allah na jefa kuria a garin Otuoke na Bayelsa ashekara ta 2011
Wata baiwar Allah na jefa kuria a garin Otuoke na Bayelsa ashekara ta 2011 AFP/ Pius Utomi Ekpei

Gwamnan jihar Edo dake Najeriya Godwin Obaseki ya lashe zaben Gwamnan da aka yi Asabar  inda ya sami zarcewa da mulkin jihar wa'adi na biyu karkashin wata jam'iyar ba wadda ya tsaya takara ba a wa'adinsa na farko.

Talla

Godwin Obaseki ya tsaya takaran ne na Asabar karkashin jam'iyar adawa ta PDP, bayan da ya sami sabanin ra’ayi da Adams Oshiomole tsohon shugaban Jam'iyar APC kuma kusa a Siyasar Jihar Edo.

Daga cikin kananan Hukumomin 18 na Jihar ta Edo Godwin Obaseki ya lashe zaben da kyakykyawan rinjaye a kananan Hukumomi 13 inda ya sami yawan kuriu 307,955 yayinda Osagie Ize-Iyamu na jamiyar APC ya sami yawan kuri'u 223,619.

Tuni dai shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya aikewa wanda yayi nasara sakon fatan alheri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.