Najeriya

An Yi Jana'izar Sarkin Zazzau Shehu Idris A Zaria

Marigayi Sarkin  Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris
Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Dr Shehu Idris YouTube

An yi Jana'izar mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris a fadarsa dake cikin ganuwar  Zaria.

Talla

Gwamnan Jihar Kaduna yana cikin mutane na farko da suka tabbatar da rasuwa da fadawa duniya ta kafofin sadarwan zamani.

Da misalin karfe biyar na yammacin Lahadi aka binne gawan marigayi Shehu Idris a cikin gidan Sarki inda aka binne wadanda suka gabaceshi.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai na daga cikin dubban jamaa da suka halarci sallar jana'iza da ya sami halarcin jama'a daga sassan Najeriya.

A farkon wannan shekaran ne  Marigayi Alhaji Shehu Idris ya cika shekaru 45 bisa gadon sarautar, inda aka yi addu'oi da rokawa kasar Nigeria zaman lafiya.

Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.