Najeriya-Boko Haram

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kisan kwamandanta a artabu da Boko Haram

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai. .elendureportsonline

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da rasuwar daya daga cikin kwamandodin ta Kanar Dahiru Chiroma Bako sakamakon artabu da mayakan boko haram a jihar Barno.

Talla

Sanarwar da mai Magana da yawun rundunar sojin Kanar Ado Isa ya sanyawa hannu ta ce kwamandan sojin Kanar Dahiru Chiroma Bako wanda ko yaushe a gaba ya ke wajen jagorancin dakarun sa wajen yaki da yan ta’adda, na jagorancin tawagar sojin ne daga Sabon Gari zuwa Wajiroko kusa da Damboa lokacin da mayakan boko haram suka masa kwantan bauna ranar lahadi da misalign karfe 10 na safe.

Sanarwar ta ce nan ta ke aka dauke shi ta jirgin sama zuwa asibitin sojin da ke rundunar ta 7 a Barikin Maimalari domin kula da shi, kuma ya fara murmurewa bayan anyi masa aiki amma yau litinin da safe bayan ya yi sallar asuba ya rasu.

Kanar isa ya ce a karkashin jagorancin kanar Bako rundunar sojin ta samu gagarumar nasara wajen murkushe yan ta’adda da kuma kwato makamai da dama.

Shugaban sojin Janar Tukur Yusuf Buratai ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwan Kanar Bako wanda ya bayyana shi a matsayin gwarzon soja da ya sadaukar da ran sa domin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.