Najeriya

Mata dubu 22 sun zama zaurawa a Zamfara

Mata da kananan yara na fuskantar wahalar rayuwa sakamakon rasuwar masu kula da su a Zamfara
Mata da kananan yara na fuskantar wahalar rayuwa sakamakon rasuwar masu kula da su a Zamfara REUTERS/Emmanuel Braun

Kimanin zaurawa dubu 22 aka samu a jihar Zamfara da ke Najeriya sakamakon kisan gillar da ‘yan bindiga suka yi wa mazajensu, lamarin da ya mayar da kananan yara akalla dubu 44 marayu kamar yadda Kungiyar Matasan Arewa ta AYF ta sanar.

Talla

Shugaban kungiyar na kasa Gambo Ibrahim Gujungu ya bayyana cewa, a cikin shekara takwas kacal aka samu wannan adadi mai tayar da hankali.

Kungiyar ta AYF ta kuma ce, ‘yan bindigan sun kashe maza magidanta akalla dubu 11 tsakanin wannan lokaci.

Gujungu ya bayyana kashe-kashen da ake fama da su a Zamfara da suka hada da sace jama’a domin karbar kudin fansa da fyade da sace shanu da lalata kadarori a matsayin abin damuwa, yana mai cewa, a can baya, yankin arewa maso yammacin Najeriya ya kasance mai zaman lafiya.

“Yana da wahala a yi kwana guda ba tare da an samu irin wannan aika-aikatar ba a yanzu” a cewar shugaban na AYF.

Kungiyar ta gargadi mummunan abin da ka iya kasance nan gaba muddin aka ci gaba da zura ido ba tare da daukar matakin da ya dace ba kan wannan batu na kashe-kashe a Zamfara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.