Atiku ya musanta zargin Amurka na sanya ido a kansa

Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya.
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban Najeriya. REUTERS/Temilade Adelaja

Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana cewar babu gaskiya dangane da zargin da ake masa cewar Amurka na sanya ido akan sa tare da iyalan sa sakamakon hada hadar kudade.

Talla

Sanarwar da mai Magana da yawun Atiku ya gabatarwa manema labarai tace, babu gaskiya cikin lamarin, domin kuwa babu wani zargi ko tuhuma da aka masa daga Amurka.

Sanarwar tace kafin zaben shekarar 2019 Atiku ya ziyarci Amurka kuma ya zauna a otel kusa da ma’aikatar tsaron kasar kuma babu abinda ya faru, inda yake danganta rahotan da yunkurin bata masa suna bayan nasarar da suka samu a zaben Gwamnan Jihar Edo.

Ko a bara an yada rahotanni cewa Amurka ta soke bai wa Atiku Bisa, saboda zargin sa da aikata laifin cin hanci da rashawa, yayin da majiyoyi ke cewa, an ba shi damar shiga kasar ne bayan wasu ‘yan siyasa sun nema masa alfarma daga wurin ‘yan Majalisar Dokokin Kasar.

Wata majiya ta shaida wa Reuters cewa, Amurka ta bude wa Atiku kofa ne saboda gudun tabarbarewar alaka da shi da zaran ya samu nasara a zaben shugabancin Najeriya wadda ta fi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.