Najeriya

Kotu ta haramtawa gamayyar kungiyar kwadago shiga yajin aiki da zanga-zanga

Shugabannin gamayyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC yayin tattakin zanga zangar adawada gwamnati a birnin Abuja
Shugabannin gamayyar kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC yayin tattakin zanga zangar adawada gwamnati a birnin Abuja Reuters

Kotun sasanta rikicin ma’aikata da ke Najeriya, ta haramtawa kungiyoyin kwadagon NLC da TUC tsunduma yajin aikin gama gari da kuma gudanar da zanga-zanga, domin nuna adawa da karin farashin man fetur da kuma wutar lantarki da gwamnatin tayi.

Talla

Alkalin kotun Ibrahim Galadima, ya bada umurnin hana kungiyoyin gudanar da ayyuka ko hana ma’aikata zuwa wuraren aikinsu har zuwa lokacin da zai saurari karar da aka gabatar masa dangane da yajin aikin.

Alkalin kotun ya kuma baiwa Sifeto Janar na 'Yan Sanda da shugaban hukumar DSS umurnin bada kariya ga duk wani ma’aikaci domin ganin yaje wurin aikinsa ba tare da tsangwama ba.

Kungiyar NLC da TUC sun bukaci gwamnatin Najeriya ta janye karin man da wutar lantarki ko kuma sun tsunduma cikin yajin aikin gama gari daga ranar litinin mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.