Najeriya

Masu satar kananan yara sun gurfana gaban kotu a Gombe

Wasu mutane da ake tuhuma dasace kananan yara daga arewacin Najeriya zuwa kudanci bayan shiga hannun 'yan sanda a jihar Kano.
Wasu mutane da ake tuhuma dasace kananan yara daga arewacin Najeriya zuwa kudanci bayan shiga hannun 'yan sanda a jihar Kano. Daily Trust

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe dake Najeriya ta gurfanar da wasu mutane 4 gaban kotu da ake zargin suna da hannu wajen sayar da kananan yara 13 da aka kaisu jihar Anambra.

Talla

Mutanen da ake tuhuma sun hada da Hauwa Usman dake garin Gombe, da Ali Bala Shaukani dake Jalingo da kuma Nkechi Nduliye dake Idemili dake Jihar Anambra, yayin da ta 4 Chioma ta tsere kamar yadda kakakin ‘yan sandan jihar ta Gombe Obed Mary Malu ta shaidawa sashin Hausa na RFI.

Kakakin ‘yan sandan jihar Gombe Obed Mary Malu kan masu satar kananan yara

Wannan dai ba shi ne karo na farko da rundunar ‘yan sandan Najeriya ke kama mutanen da ke sace kananan yara daga arewacin kasar suna sayar da su a kudancin kasar ba, inda ake sauya musu suna da kuma addini.

Cikin watan Fabarairun wanna shekara, rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta gano wani gida da ake ajiye yaran da aka sato, kafin cin kasuwarsu.

Rahotanni kuma sun ce har yanzu akwai kimanin karin yara 70 dake ake cigaba da bincike don gano inda suke, abinda ya sanya gwamnatin Kano ta kafa wani kwamiti, da ta baiwa alhakin tantancewa tare da lalubo inda aka saida sauran yaran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.