Najeriya-Borno

Adadin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe a tawagar Zulum ya karu

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum tare da tawagar jami'ansa.
Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum tare da tawagar jami'ansa. RFI Hausa

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon farmakin da mayakan Boko Haram suka kaiwa tawagar motocin gwamnan jihar Borno Babagana Zulum a ranar Juma’a ya karu, daga 15 zuwa 30.

Talla

Alkaluman da suka soma fita da fari dai sun nuna cewar jami'an tsaro 15 kawai mayakan suka kashe, inda shi kuma gwamnan na Borno ya tsira ba tare da samun rauni ba.

Wakilinmu Bilyaminu Yusuf da ke Maiduguri ya shaida mana cewar an kaiwa tawagar motocin gwamnan na Borno farmaki ne a kauyen Korochara mai nisan kilomita 2 daga garin Baga inda hedikwatar rundunar hadin gwiwar sojin dake yakar kungiyar Boko Haram take.

Wakilin namu ya ce gwamnan na Borno da tawagar sa na kan hanyar isa garin na Baga dangane da shirin maida 'yan gudun hijira zuwa gidajensu, kamar yadda za a ji a tattaunawarsu da Ahmad Abba.

Mayakan Boko Haram sun yi tawagar gwamnan Borno kwanton Bauna

Sa'o'i bayan zantawa da Bilyaminu ne, wasu majiyoyi suka shaidawa kamfanin dillacin labarai na AFP cewar adadin mutanen da suka rasa rayukansu a harin na Boko Haram ya kai 30, ciki har da jami’an tsaro da suka hada da sojoji, .yan sanda, da kuma Civilian JTF 4.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI