Najeriya

Buhari ya yi Allah-wadai harin Boko Haram kan gwamnan Borno

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP/SAUL LOEB

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, yayi Allah-wadai da farmakin da mayakan Boko Haram suka kaiwa tawagar motocin gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, harin da yayi sanadin mutuwar jami’an tsaro da dama da suka hada da ‘yan sanda da kuma jami’an Civilian JTF.

Talla

Shugaba Buhari ya bukaci gwamnan na Borno da ya cigaba da jajircewa kan shirinsa na maida ‘yan gudun hijirar da suka tserewa hare-haren mayakan Boko Haram zuwa garuruwansu.

Buhari ya kuma bayyana harin da aka kaiwa tawagar gwamnan a gaf da garin Baga a matsayin shiryayyar manufa ta wargaza shirin maida mutane zuwa garuruwansu da a baya suka tserewa saboda rashin tsaro.

Yanzu haka dai adadin mutanen da suka mutu sakamakon a farmakin na Boko Haram a ranar Juma’a ya karu, daga 15 zuwa 30, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Wakilinmu Bilyaminu Yusuf da ke Maiduguri ya shaida mana cewar an kaiwa tawagar motocin gwamnan na Borno farmaki ne a kauyen Korochara mai nisan kilomita 2 daga garin Baga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.