Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan sanda sun kama mutane 5 da suka yi wa yarinya fyade a Bauchi

Mutane 5 sun yi wa yarinya mai shekaru 14 fyade a Bauchi
Mutane 5 sun yi wa yarinya mai shekaru 14 fyade a Bauchi Reuters
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Bauchi ta sanar da damke mutane 5 da suka yi wa wata yarinya mai shekaru 14 fyade.

Talla

Kakakin ‘yan sandan a Bauchi DSP Ahmed Wakil, ya ce mutanen sun shiga hannu ne a ranar 22 ga watan Satumban da muke a kauyen Udubo dake karamar hukumar Gamawa, bayan samun cikakkun bayanan cewa, masu laifin da ke tsakanin shekaru 22 zuwa 32 sun yi wa yarinyar fyade a lokuta da dama, inda suka rika bata naira 200 zuwa 500.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewar dukkanin mutanen sun amsa aikata laifin, kuma cikinsu har wani da jami’an tsaro suka dade suna farautarsa bisa wani laifin na dabam da ya aikata na fyaden.

Matsalar yiwa kananan yara fyade dai na cigaba da yawaita a sassan kasar, la’akari da cewar a cikin watan nan aka kama wani dattijo yana wa wata karamar yarinya fyade cikin Masallaci a dai garin na Bauchi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.