Addu'a ce za ta ceto Najeriya daga barazanar rushewa- Osinbajo

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo.
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo. Afolabi Sotunde/Reuters

Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya yi gargadin cewar Najeriya na fuskantar rugujewa, inda ya bukaci al’ummar kasar da su cigaba da addu’a da kuma jajircewa wajen ganin ta dore.

Talla

Osinbajo wanda ke jawabi a Mujami’a ta kasa da ke Abuja, dangane da bikin cika shekaru 60 da samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, ya ce har yanzu akwai fata mai kyau duk da ya ke wani sashe na ginin kasar ya fara tsagewa.

Mataimakin shugaban kasar ya ce Najeriya na bukatar wani manzo a yau domin tinkarar dimbin matsalolin da suka addabi kasar duk da tsananin adawar da zai gamu da su.

Yayin da ya ke bayyana fatar ganin cika shekaru 60 zai bude wani sabon babi a kasar, Osinbajo ya bayyana cewar babu wata kungiya da ta ke shirye wajen tinkarar wadannan matsaloli da ta wuce ta addinai.

Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, Samson Ayokunle ya jadadda cewar adalci shi ne kawai zai tabbatar da zaman lafiya da son juna a cikin kasar.

Ayokunle ya ce muddin ana bukatar hadin kai da tafiya tare, ya zama wajibi a tabbatar da daidaito wanda zai baiwa kowa damar samun aikin yi da shugabanci na gari da kuma ilimi a fadin kasa.

Shugaban kiristocin ya ce ya dace a dama da kowanne sashe na kasar nan kan batutuwan da suka shafi Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.