Isa ga babban shafi

Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun janye shiga yajin aiki

Kungiyoyin Kwadago a Najeriya sun sanar da janye yajin da suka shirya farawa domin tilastawa gwamnati janye Karin farashin mai da wutar lantarki.
Kungiyoyin Kwadago a Najeriya sun sanar da janye yajin da suka shirya farawa domin tilastawa gwamnati janye Karin farashin mai da wutar lantarki. Daily Trust
Zubin rubutu: Ahmed Abba
Minti 1

Kungiyoyin Kwadago a Najeriya sun sanar da janye yajin da suka shirya farawa yau domin tilastawa gwamnati janye Karin farashin mai da wutar lantarki, saboda abinda suka kira kuncin da ya jefa jama’ar kasa.

Talla

Bayan kwashe daren Lahadi ana tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, ministan kwadago Chris Ngige yace sun amince a dakatar da Karin wuta na makwanni biyu domin sake duba matsalar, yayin da za’a cigaba da aiwatar da Karin farashin man.

Sai dai yace gwamnati zata duba hanyoyin taimakawa ma’aikata radadin Karin.

Shugaban kungiyar kwadago ta TUC Quadri Olaleye yace sun dakatar da yajin ne domin baiwa gwamnati dama, amma ba wai janye shi gaba daya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.