Majalisar dokokin Osun na binciken wawure € 10,000 a cinikin Ighalo

Tsohon dan wasan Najeriya Odion Ighalo
Tsohon dan wasan Najeriya Odion Ighalo Getty Images

Majalisar dokokin jihar Osun a Najeriya, ta fara bincike kan bacewar wasu kudi har € 10,000 wanda ke matsayin rabon kungiyar kwallon kafar Osun United cinikin kudin da aka sayo dan wasan gaban Najeriya, Odion Ighalo daga kungiyar China ta Shanghai Shenhua zuwa Manchester United a watan Janairun wannan shekara, amma sai wasu suka karkatar da shi zuwa aljihun su.

Talla

Osun United da ke Osogbo da aka fi sani da Prime FC, ita ce kungiya ta karshe da tsohon dan wasan Super Eagles Ighalo ya buga mata wasa kafin ya koma kasashen waje, inda ya fara wasa a wani club din kasar Norway a shekarar 2007.

Wasu majiyoyi da ke kusa da kulob din sun ce Kwamishinan Wasanni na Jihar Osun, Yemi Lawal, na daga cikin wadanda aka gayyata zuwa zauren Majalisar a makon da ya gabata kan batun.

Kazalika ganawar Majalisar wanda Shugaban kwamitin wasanni, Adrullahi Adegbile ya jagoranta, ya samu halartan jami’ai na Osun United, karkashin jagorancin sakataren kungiyar, Kabiru Adekunle, da mukaddashin Janar Manajan Hukumar Wasanni ta Jihar Osun, Rotimi Oludun-moye.

Har ila yau, cikin wadanda ake zargi da karkata kudaden harda Gbenga Ololade, tsohon Babban Manajan riko na Prime FC, wanda ke jagorantar club din a lokacin, da aka kulla yarjejeniyar cikin Ighalo.

Shugaban kwamitin wasanni na majalisar dokokin Osun, Adegbile, ya ce har yanzu kwamitin bai kammala bincikensa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.