Najeriya ta kera na'urar gwajin korona mai bada sakamako cikin mintuna

Najeriya ta kera na’urar gwajin cutar korona
Najeriya ta kera na’urar gwajin cutar korona AP Photo/Charles Krupa

Gwamnatin Najeriya ta sanar da samun nasarar kera na’urar gwajin cutar korona da ta kera a cikin gida wanda kan iya bada sakamakon gwaji cikin mintuna 40 kacal.

Talla

Karamin ministan lafiya Olorunnimbe Mamora ya sanar da nasarar wajen ganawa da manema labarai kan halin da ake ciki wajen yaki da cutar.

Mamora yace Cibiyar Bincike da Nazarin magunguna ce ta kera na’urar wanda zai taimakawa kasar wajen cigaba da gwaji ga marasa lafiya.

A baya-bayan nan dai Najeriya mafi karfin tattalin arziki a Nahiyar Afrika ta fara kulle wasu cibiyoyin gwajin cutar korona bayan da ta ke ci gaba da samun raguwar sabbin kamuwa da cutar a sassan kasar, a dai-dai lokacin da cutar Covid-19 din ke tsananta a wasu sassan Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.