Birtniya-Najeriya

Sarauniyar Ingila ta yi wa Najeriya barkar cika shekaru 60

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II
Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II Wikimedia commons/CC By 2.0

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta aike da sakon taya murna ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da kuma jama’ar kasar dangane da bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai da zai gudana a gobe 1 ga watan Oktoba na shekarar 2020.

Talla

Babban jami’in diflomasiyar Birtaniya da ke Najeriya ya gabatar da sakon taya murnar da kuma fatar alheri daga Sarauniyar wadda ta yi wa kasar fatar samun ci gaba da kuma kwanciyar hankali.

Elizabeth ta bayyana cewar kasashen Najeriya ta Birtaniya sun ci moriyar dangantaka a matsayin ‘ya'yan kungiyar kasashe renon Ingila ta fannin tarihi da kuma jama’ar da ke cikin kasashen, inda ta bayyana fatar ci gaba da dorewarsa.

Najeriya ta samu yancin kai ne daga Birtaniya ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 1960.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.