Zankai Najeriya wasan Quater finals a gasar kofin duniya mai zuwa - Rohr

Tsohon dan wasan Najeriya John Obi Mikel da cocin tawagar yanzu haka Gernot Rohr.
Tsohon dan wasan Najeriya John Obi Mikel da cocin tawagar yanzu haka Gernot Rohr. REUTERS/MATTHEW CHILDS

Manajan tawagar super Eagles ta Najeriya, Gernot Rohr yace burin da ya rage masa a harkokin horarwa a Afirka yanzu haka shine samun tikitin gasar neman cin kofin duniya na Qatar 2022, tare da isa har zagayen wasannin daf da na kusa da na karshe wato Quarter finals.

Talla

Cocin na Super Eagles ya bayyana wannan buri nasa a wata hira ta musamman da yayi da mujallar wasanni ta FIFA.com, kan rawar da ya taka a horas da ‘yan wasa na kungiyoyi da kasashen nahiyar Afirka.

Rohr wanda yayi tsokaci kan ritayan wasu fitattun ‘yan wasan Super Eagles irinsu Moses da Mikel Obi da Ighalo, a matsayin mutanta matsayinsu, yace akwai ‘yan wasa da zasu nuna bajinta wajen cimma wannan buri nasa, ta hanyar doke takwarorinsu da ke rukuni guda da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.