Najeriya

'Yan siyasar Najeriya na da babban laifi-Janar Abdulsalam

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdusalam Abubakar ya bayyana cewa, 'yan siyasar kasar na tafka babban laifi saboda yadda suke bai wa matasa kwayoyi da makamai musamman a lokutan zabe domin cimma muradunsu a siyasance.

Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya Janar Abdusalam Abubakar
Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya Janar Abdusalam Abubakar Channelstv
Talla

Janar Abdulsalam ya bayyana haka ne a yayin zantawa da manema labarai kan bikin cika shekaru 60 da Najeriya ta samu 'yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar tsohon shugaban na Najeriya.

'Yan siyasar Najeriya na da babban laifi-Janar Abdulsalam

Janar Abdulsalam shi ne wanda ya jagoranci mika mulki ga farar hula da ake cin gajiyarsa a yau, inda ya mika mulki ga Olusegun Obasanjo bayan ya lashe zaben da aka gudanar karkashin tsarin dimokradiya a shekarar 1999.

Kodayake tsohon shugaban ya bayyana cewa, Najeriya ta samu ci gaba a cikin tsawon shekaru 60 da karbar 'yancin cin gashin kanta daga Turawan Birtaniya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI