Najeriya

Bai kamata Buhari ya kwatanta farashin man Najeriya da Saudiya ba- TUC

Hadakar Kungiyar Kwadaon Najeriya ta TUC ta caccaki yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kwatanta kasar da Saudi Arabia a bangaren farashin da al'umma ke sayen man fetur.

Wata tashar sayar da man fetur a Najeriya.
Wata tashar sayar da man fetur a Najeriya. REUTERS/ Afolabi Sotunde
Talla

A yayin gabatar da jawabinsa na bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, shugaba Buhari ya ce, rashin hikima ne farashin man fetur ya yi araha a Najeriya fiye da a Saudi Arabia, kalaman da ke ci gaba da janyo cece-kuce a sassan kasar.

Shugaban TUC, Quadri Olaleye ya ce, bai kamata shugaban ya yi wannan kwatance ba saboda Saudiya ta zarta Najeriya ta fannoni da dama na inganta rayuwar al’ummarta.

Yanzu haka dai al'ummar Najeriyar na sayen duk lita guda ta man fetur kan Naira 157 zuwa 161 inda su ke karbar Naira dubu 30 a matsayin mafi karancin albashi yayinda Saudi Arabia ke sayar da litar man kan Naira 168 amma al'ummarta ke karbar Naira dubu dari 3 a matayin mafi karancin albashi.

Tuni dai al'ummar Najeriyar ke ci gaba da mayar da martani kan kalaman na Buhari, inda suka bukaci ya yi kokarin daidaita mafi karancin albashin ma'aikatan kasar da na Saudiya gabanin daidaita farashin man.

Bayan kai ruwa rana na tsawon shekaru tsakanin gwamnatin Najeriyar da kungiyoyin kwadago ne aka iya mayar da mafi karancin albashin ma'aikatan kasar zuwa Naira dubu 30, dai dai da farashin da ake sayar da buhun shinkafa a sassan kasar mai arzikin man fetur, sai dai duk da hakan jihohi da dama sun ki amincewa da karin a aikace.

Kalaman na Muhammadu Buhari ya janyo masa kakkausar suka daga al'ummar ta Najeriya dai dai lokacin da ake tsaka da fuskantar matsalolin rayuwa da suka kunshi tashin farashin kayakin masarufi, matsin rayuwa, hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa wanda ya hana noma a garuruwa da dama baya ga ambaliyar ruwa da ke ci gaba da shanye gonaki da kuma uwa uba rashin aikin yi da ya yiwa matasan kasar katutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI