Najeriya

Najeriya ta yi umarnin bude makarantu a dukkan matakai

Wasu daliban firamare a wata makaranta da ke birnin Abuja, Najeriya.
Wasu daliban firamare a wata makaranta da ke birnin Abuja, Najeriya. NTA.ng

Gwamnatin Najeriya ta yi umarnin bude ilahirin makarantun kasar da ke kowanne mataki bayan kasancewarsu a rufe kusan watanni 8 saboda fargabar annobar Coronavirus da ta lakume rayukan mutum dubu 1 da 112 a fadin kasar.

Talla

Majiyar labarai a Najeriyar ta ruwaito ministan ilimin kasar Malam Adamu Adamu na umartar bude ilahirin makarantun yayin wani taron manema labarai da ya kira a Abuja yau Juma’a a Abuja.

Ministan Ilimin ya bukaci kowacce makaranta a kowanne mataki ta mutunta dokokin da aka gindaya na bude makarantun don kare lafiyar dalibanta daga kamuwa da cutar ta Coronavirus.

Malam Adamu Adamu ya sanar da ranar 12 ga watan Oktoban da muke ciki wato nan da kwanaki 10 masu zuwa a matsayin ranar da makarantun da ke karkashin gwamnati na ‘‘Unity’’ za su koma, yayinda ya bukaci makaranta masu zaman kansu su kammala tsare-tsaren kiyaye lafiyar dalibai gabanin komawa karatu.

Many states including Lagos, Oyo, Kano and Enugu, have since announced dates for the reopnening of schools in their states.

Kafin umarnin Ministan dai tuni jihohin Lagos Oyo da Kano baya ga Enugu suka sanar da ranar da makarantu za su bude don ci gaba da karatu.

Tun cikin watan Maris din da ya gabata ne gwamnatin Tarayyar Najeriyar ta yi umarnin kulle ilahirin makarantun kasar tun daga matakin Firamare zuwa Jami’a don dakile yaduwar cutar ta coronavirus wadda zuwa yanzu ta harbi mutane dubu 59 a jihohin kasar 36 da birnin Tarayya Abuja ko da ya ke mutum dubu 50 yanzu haka sun warke daga cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI