BUK ta jagoranci farfado da noman gyada a Najeriya
Wallafawa ranar:
Cibiyar nazarin ayyukan noma ta Jami’ar Bayero da ke Najeriya ta ja ragamar farfado da noman gyada da kuma dawo harkar a sassan arewacin kasar.
Rahotanni sun ce, tuni aka fara noman gwaji a wani fili da girmansa ya kai kadada 50 a Kano tare da taimakon cibiyar domin inganta noma nau’i daban daban na gyadar ga manoma.
Gyada na daya daga cikin manyan hajojin da ke samar wa Najeriya kudaden shiga kafin gano man fetur a shekarar 1970, kuma tun bayan lokacin noman gyadar ya samu tasgaro, yayin da hukumomi da manoma suka yi watsi da ita.
Mataimakin Daraktan Cibiyar, Farfesa Sanusi Gaya ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewar, sun yi nasarar samar da nau’ukan gaydar har guda 9 daga Cibiyar Binciken Ayyukan noma na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
Farfesa Gaya ya ce manoma da dama sun yi gwajin wasu daga cikin nau’ukan gaydar kuma sun yaba da abin da suka gani.
Masanin harkar noman ya bukaci manoma su rungumi amfani da irin gaydar da suka samar wadanda aka inganta domin amfaninsu ga jama’a baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu