Najeriya

Chevron zai sallami kashi 25 na ma'aikatansa a Najeriya

Kamfanin Mai na Chevron da ke aikin hadin gwuiwa da NNPC a Najeriya ya bayyana cewar zai sallami kashi 25 na ma’aikatansa, kuma tuni ya fara nazari kan wadanda za a kora daga aikin.

Kamfanin mai na Chevron na aiki ne tare da hadin guiwar NNPC na Najeriya.
Kamfanin mai na Chevron na aiki ne tare da hadin guiwar NNPC na Najeriya. Getty Images/Justin Sullivan
Talla

Janar Manajan da ke kula da manufofin kamfanin da kuma hulda da jama’a, Esimaje Brikinn ya bayyana haka inda yake cewa kamfanin na duba hanyoyin da zai rage kashe kudade wajen gudanar da harkokinsa na yau da kullum.

Manajan ya ce matakin da suke dauka zai taimaka wajen kara kaimi da kuma tabbatar da ingancin ayyukan kamfanin tare da rage kudin da ake kashewa da kuma kara ribar da yake samu.

Brikinn ya musanta zargin da cewar kamfanin na kokarin sallamar ma’aikatan ne domin mayar da ayyukan zuwa wasu kasashe, inda ya kara da cewar matakin da suke dauka ya danganci halin da duniya take ciki a yau da kuma bukatar daukar matakai masu karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI