Najeriya

An kaddamar da shirin zaman lafiya a Zangon-Kataf

Al'umomin da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kadunan Najeriya sun kaddamar da shirin zaman lafiya wanda ake sa ran zai kawo karshen tashe-tashen hankulan da suka addabi yankin.

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'. kdsg.gov.ng
Talla

Shirin wanda ke zuwa a karkashin babban Basaraken Masarautar Atyap ya kunshi kwamitin mutane 80 da suka fito daga kabilun da ke zaune a karamar hukumar.

Yayin kaddamar da kwamitin, Basaraken Agwatyap Dominic Yahaya ya ce kwamitin ya biyo bayan daya daga cikin yarjejeniyar da aka kulla bayan taron da ya gudana a ranar 22 ga watan Agusta, matakin da ya haifar da zaman lafiya a yankin.

Basaraken ya ce a ci gaba da lalubo hanyar samun dawamammen zaman lafiya, ya zama wajibi a aiwatar da daukacin yarjeniyoyin da aka kulla bayan taron zaman lafiyar da aka yi domin ganin sun yi aiki a kowanne sako da ke karamar hukumar, saboda haka aka kafa wannan kwamiti na tsaro da zaman lafiya a yankin.

'Yan kwamitin sun fito daga kabilar Kataf da Hausawa da Fulani da Igbo, kuma sun kunshi Musulmi da Kiristoci da matasa da mata da kuma wakilan kungiyoyin fararen hula na Miyetti Allah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI