Mun yi wa Boko Haram luguden wuta-Sojin Najeriya
Wallafawa ranar:
Shalkwatan Tsaron Najeriya ya bayyana cewa, dakarunsa na Operation Lafiya Dole sun sake samun nasarar fatattakar mayakan Boko Haram a sansanoninsu da ke yankin arewa maso gabashin kasar.
Jami’in Yada Labaran Shalkwatan, Manjo Janar John Eneche ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar yau Asabar a birnin Abuja.
Jami’n ya ce, a ranar 1 ga watan Oktoban nan, sojojin suka fatattaki mayakan daga maboyarsu ta Maima da Tusuy da ke kusa da Warshale da kuma Tongule a jihar Borno.
Dakarun sun yi amfani da jiragen sama na yaki wajen kaddamar da farmaki kan mayakan na Boko Haram a cewar sanarwar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu