Najeriya

An haramta wa rundunar SARS binciken 'yan Najeriya

An kirkiri rundunar 'yan sandan SARS ne domin yaki da gaggan barayi a Najeriya.
An kirkiri rundunar 'yan sandan SARS ne domin yaki da gaggan barayi a Najeriya. Premium Times

Babban Sufeta Janar na ‘Yan sandan Najeriya, Mohd. Adamu ya haramta wa rundunar yaki da gaggan barayi da aka fi sani da Federal SARS aikin sintiri da kuma binciken jama’a a shingen ababan hawa.

Talla

Sanarwar da ta fito daga ofishin Babban Sufetan ‘Yan sandan ta kuma ce, daga yanzu dole ne jami’an SARS suka rika sanya tufafinsu wato Uniform.

Wannan na zuwa ne bayan dimbin rahotanni sun tabbatar cewa, jamian na fakewa da karfin da aka ba su wajen aikata miyagun laifuka da suka saba wa tsarin aikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.