Najeriya - Buhari

Buhari ya amince da albashi na musamman ga malamai

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Nigeria/presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da wani tsarin biyan albashi na musamman ga malaman makarantu, matakin da zai banbanta su da sauran ma’aikatan gwamnati.

Talla

A karkashin wannan tsari, shugaban ya kuma amince da tsawaita lokacin aikin malaman daga shekaru 35 zuwa 40 domin baiwa dalibai damar cin moriyar kwarewar malaman.

Ministan ilimi Adamu Adamu ya sanar da wadannan matakan wajen bikin ranar malamai ta duniya dake gudana a Abuja.

Adamu yace shugaban kasar ya bashi umurnin tababbatar da aiwatar da sabon tsarin albashi domin taimaka musu wajen ganin su sauke nauyin dake kan su.

Malaman makarantu a Najeriya na daga cikin wadanda basa samun kular da ta dace wajen ganin sun gudanar da ayyukan su, abinda ya sa kwararru daga cikin s uke barin aikin suna komawa wasu bangarori na daban.

Wannan ya sa makarantu ke dibar malaman da basu da kwarewa domin gudanar da aikin malantar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.