Gwamnati ta gargadi 'yan Najeriya kan yi mata bore
Wallafawa ranar:
Gwamnatin Najeriya ta gargadi al’ummar kasar da su nesanta kansu daga masu shirya zanga-zangar adawa da gwamnati irin wadda aka yi a shekarar 2012 domin nuna bacin rai da yadda ake gudanar da mulkin kasar.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Femi Adeshina ya bayyana masu daukar nauyin zanga-zangar a matsayin abokan gabar kasar da ke neman jefa ta cikin halin tashin hankali domin neman biyan bukatar kansu.
Adeshina ya ce tun bayan da kungiyoyin kwadagon kasar suka rungumi hanyar sulhu da kuma tattaunawa wajen gamsuwa da dalilan da gwamnati ta gabatar kan dalilin kara farashin mai da kudin wutar lantarki kana bude kofar ci gaba da ganawa a tsakanin bangarorin biyu, wasu mutane da ba sa bukatar ganin ci gaban kasar suka fara nuna rashin amincewarsu da matakin.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce wadannan mutane sun shirya tsaf domin yin amfani da yajin aikin ma’aikatan wajen cimma muradun kansu ta hanyar tinzira jama’a su bijire wa gwamnati amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba, abin da ya sa suka koma caccakar kungiyoyin kwadagon kasar.
Adeshina ya yaba wa kungiyoyin kwadagon kasar kan halin dattakon da suka nuna wanda ya kai ga kauce wa yajin aikin da zai mayar da hannun agogo baya.
Mai magana da yawun fadar shugaban ya bayyana mutanen a matsayin wadanda suka sanya neman mulki ta kowacce hanya a gaba, ba tare da son Najeriya ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu