Najeriya

'Yan sandan Najeriya na ba-haya a daji saboda rashin makewayi'

Wasu daga cikin 'yan sandan Najeriya
Wasu daga cikin 'yan sandan Najeriya Getty Images

A yayin da 'yan Najeriya ke mayar da martani kan matakin da Babban Sufetan 'yan sandan kasar, Mohammed Adamu ya dauka na haramta wa rundunar yaki da gaggan barayi wato SARS binciken jama'a a shingayen ababan hawa, daya daga cikin jami'an Hukumar Daukar 'Yan sanda ta bayyana cewa, rashin bai wa 'yan sandan cikakkiyar kulawa ke tilasta musu shiga daji domin biyan bukatarsu ta ba-haya, yayin da ba sa samun ingantaccen abinci.

Talla

A zantawarta da Sashen Hausa na RFI, Hajiya Naja'atu Mohammed ta yaba da matakin dakatar da dakarun rundunar SARS saboda yadda suke wuce gona da iri wajen keta hakkokin al'umma.

Naja'atu ta ce, akwai korafe-korafe da yawa kan rundunar SARS dangane da kisan mutane ba bisa ka'ida ba da kuma karbe dukiyar al'umma a shingayen binciken ababan hawa.

Kodayake Naja'atu ta ce, 'yan sandan na SARS na gudanar da aiki mai kyau amma badakalar zaluntar al'umma ta fi yawa a aikinsu.

Sai dai a lokacin da take tsokaci kan kula da hakkokin 'yan sanda da kudadensu na alawus-alawus, Naja'atu ta ce, babu wani abin kirki da aka yi musu, ganin yadda suke rayuwa cikin mawuyacin hali, ciki har da shiga daji don yin ba-haya saboda rashin makewayi, sannan kuma ba sa samun ingantaccen abinci.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da muka yi da ita kan wannan batu.

 

'Yan sandan Najeriya na ba-haya a daji saboda rashin makewayi'

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.