Najeriya

Kaduna na shirin karkasa sarautar Zazzau

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai. Daily Post

Yayin da ake ci gaba da dakon nada wanda zai gaji tsohon Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta sanar da shirin gabatar da wata doka a Majalisa wadda za ta sake fasalin Majalisar Sarakunan Jihar Kaduna.

Talla

Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta ce matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewar gwamnan jihar Nasir El Rufai na shirin karkasa Masarautar Zazzau zuwa gida 3 domin nada fitattun ‘ya'yan Sarki 3 da ke sahun gaba wajen neman sarautar Zaria.

Jarida ta ce idan majalisa ta amince da dokar, Magajin Garin zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli zai zama Sarkin Kaduna, yayin da Yariman Zazzau Alhaji Muhammadu Mannir Jafaru zai zama Sarkin Zazzau, sai kuma Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu ya zama Sarkin Kudan.

Yayin gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa, gwamna El Rufai ya tabbatar da kudirin dokar wadda ya ce nan gaba kadan za a mika wa majalisar dokokin kamar yadda Jaridar ta bayyana.

Allah Ya yi wa mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris rasuwa ne ranar 20 ga watan jiya bayan gajeruwar rashin lafiya a asibitin Kaduna yana da shekaru 84 a duniya.

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da sunayen farko da masu zabar Sarkin Zazzau suka gabatar domin nada wanda zai maye gurbin tsohon sarki saboda abin da ta kira gabatar da rahotan ga jama’a kafin gwamnati ta yanke hukunci a kai.

Sai dai rahotannin da ke zuwa yanzu na cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta musanta wannan batu na karsasa masarautar Zazzau kamar yadda Kwamishin Tsaron Jihar Samuel Aruwan ya shaida wa wakilinmu Aminu Sani Sado.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.