Najeriya

Najeriya za ta haramtawa jirage marasa rijista shawagi a ruwanta

Hukumar kula da sufirin ruwa ta Najeriyar ta bai wa jiragen wa'adin watanni 3 don su kammala rijista tare da sabunta lasisi.
Hukumar kula da sufirin ruwa ta Najeriyar ta bai wa jiragen wa'adin watanni 3 don su kammala rijista tare da sabunta lasisi. Reuters

Najeriyan ta sanar da shirin haramtawa jiragen ruwa marasa rijista shawagi a ruwanta yayinda da ta bai wa kamfanonin da ke hada-hadar kasuwanci da jiragen na ruwa wa’adin watanni 3 don su gaggauta yin rijista.

Talla

Hukumar da sufurin ruwa ta Najeriyar NIMASA a sanarwar da ta fitar makon nan, ta ce za ta sanar da kamfanonin main a ketare kan su dakatar da hada-hada tsakaninsu da kamfanonin marasa rijista daga Najeriyar.

Galibin jiragen da ke shawagi a ruwan Najeriyar wadanda galibinsu mallakin ‘yan kasuwa ne, na aikin safarar danyen man fetur ne zuwa kasashen duniya.

Sanarwar ta NIMASA ta ce wa’adin na watanni 3 ya shafi hatta kamfanonin da ke da rijista amma wa’adin lasisinsu ya kare.

Matakin Najeriyar dai na zuwa ne bayan kokarin da gwamnatin kasar ke yi na ganin ta habaka kudadem shigar da ta ke samu da kuma wadatuwar kudaden musaya na ketare da rashin ya kassara bangaren musaya dai dai lokacin da darajar kudin kasar ke kara sauka.

Haka zalika mataki na zuwa dai dai lokacin da bangaren man wanda ke matsayin babbar hanyar samun kudin shigar Najeriyar ke fuskantar barazana biyo bayan annobar Covid-19.

Tarin jiragen ruwan kasashen ketare ne dai yanzu haka ke aikin safarar mai a Najeriyar ba tare da cikakken lasisi ko biyan kudaden da doka ta tanada ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.