Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Farfesa Aminu Ladan Sharehu kan matakin Buhari na kara albashi da shekarun Malamai a bakin aiki

Wallafawa ranar:

Gwamnatin Nigeria ta sanar da daukan wasu jerin matakai don kyautata rayuwar malaman makarantu a fadin kasar, albarkacin ranar Malamai da aka yi jiya. Cikin jerin kyautatawan da aka yiwa malamai har da kara yawan shekarun da za su yi bakin aiki daga 35 zuwa 40, sai kuma gyatta masu tsarin albashi da niyyar maido da kimar malunta.Mun nemi ji daga bakin Farfesa Aminu Ladan Sharehu, Matawallen Zazzau, tsohon Babban Daraktan Cibiyar Horas da Malamai a Nigeria, ko sun gamsu da matakan kyautatawa malaman yanzu.

Wani Malami yayin bayar da darasi a Aji.
Wani Malami yayin bayar da darasi a Aji. Reuters
Sauran kashi-kashi