Gwamnatin Kaduna ta nada Amb Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Gwamnatin Jihar Kaduna dake Najeriya Malam Nasir El Rufai ya nada Magajin Garin Zazzau Alh Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 domin maye gurbin Dr Shehu Idris da Allah Ya yiwa rasuwa a watan jiya.
An dai haifi Sabon Sarkin ne ranar 8 ga watan Yunin shekarar 1966 daga gidan Sarautar Mallawa kuma shi ke rike da kujerar Magajin Garin Zazzau kafin wannan nadi.
Sabon Sarkin ya halarci makarantun Firamare da Sakandare a birnin Kaduna, kafin ya tafi Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ya samu digiri a bangaren shari’a kana ya kware a matsayin lauya.
Sabon Sarkin yayi karatun digiri na biyu a Jami’ar Ahmadu Bello kafin ya tafi jami’ar Havard da Oxford da Northwestern dake Chicago da kuma Jami’ar Pennsylvannia.
Sarkin na 19 ya rike mukamai da dama ciki har da shugaban Hukumar buga kudade ta Najeriya da Jakadan Najeriyar a Thailand.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu