Najeriya

An sace shugaban karamar hukuma a Zamfara

'Yan bindiga sun dauki tsawon lokaci suna cin karensu babu babbaka a Zamfara
'Yan bindiga sun dauki tsawon lokaci suna cin karensu babu babbaka a Zamfara The Guardian Nigeria

An sace shugaban Karamar Hukumar Bakura da ke mazabar Gamji ta jihar Zamfara a Najeriya wato Sani Dangwaggo na Jam'iyyar APC mai mulkin kasar.

Talla

Majiyar iyalansa ta ce, da misalin karfe 11 na daren da ya gabata wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da shi daga gidansa da ke unguwar Gamji a daidai lokacin da ake shatata ruwan sama.

Sakataren Yada labaran Jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Shehu Isa ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa, masu garkuwar sun tuntubi iyalansa, inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

Garkuwa da mutane don karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya, matsalar da har yanzu hukumomin kasar suka gaza magance ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.