Najeriya

Kusan rabin kasafin kudin Najeriya na badi zai tafi bangaren manyan ayyuka

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Nigeria/presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa na naira triliyan 13 a zauren Majalisar dokoki, inda ya bukaci dorewar hadin kan da ke tsakanin bangarorin biyu domin yiwa kasa aiki.

Talla

Kasafin da aka tsara shi akan farashin gangar mai Dala 40 da kuma fatar fitar da ganga kusan miliyan 2 zuwa kasuwa kowacce rana, na dauke da sama da naira triliyan 5 da rabi na gudanar da manyan ayyuka da kusan naira triliyan 4 na albashi tare da biyan bashin sama da naira triliyan 3.

Daga cikin bangarorin da suka samu kaso mai tsoka a kasafin, akwai bangaren majalisa da ya samu naira biliyan 128 sai bangaren shari’a da ya samu naira biliyan 110, sai ilimin firamare da ya samu naira biliyan 70, sai Hukumar zabe da ta samu naira biliyan 40 sai kuma kamfanin NNPC da ya samu naira biliyan 29 da rabi.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sha alwashin magance koma bayan tatatlin arzikin da kasar ta fuskanta sakamakon annobar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.