Kotun a Najeriya ta bukaci rataye wani matashi da ya kashe mata 9

A Najeriya, wata kotu birnin Fatakwal ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya kan wani mutum da ta samu da laifukan yiwa mata akalla 9 kisan gilla.

Alamar kotu
Alamar kotu thisdaylive.com
Talla

Baya ga kisan gilla mai shari’a Adolphus Enebeli da ya yanke hukuncin ya kuma samu mai laifin da yunukurin halaka wata matar da aka sakaye sunanta, wadda jami’an tsaro suka ce ta yi batan dabo, duk da cewar sun bukaci ta bayyana a gaban kotun domin bada shaida.

Masu gabatar da kara sun ce Gracious David mai shekaru 40 ya rika kashe matan ne bayan amfani da su, ta hanyar sake su a dakunansu na Otal da ke garin na Fatakwal, a tsakanin watannin Yuli zuwa satumban shekarar 2019.

‘Yan sanda sun kara da cewar mai laifin ya amsa kashe 6 daga cikin matan guda 9 da ake tuhumarsa da yi musu kisan gilla, kuma mafi akasarinsu mata ne masu zaman kansu.

A ranar 19 ga satumban da ya gabata jami’an tsaro suka cafke Gracious David a lokacin da yake kokarin tserewa daga birnin Fatakwal z uwa Akwa Ibom, bayan da kamarorin tsaro ta dauki hotonsa, yayin ficewa daga daya daga cikin otal din da ya aikata kisan gilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI